'Yan gudun hijira na mutuwa a Kamaru

Kananan yara 36 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutattuka a sansanonin 'yan gudun hijira.
Bayanan hoto,

Kananan yara 36 ne suka mutu sakamakon kamuwa da cutattuka a sansanonin 'yan gudun hijira.

Rahotanni daga yankin Minowa a Jamhuriyar Kamaru sun ce 'yan gudun hijira daga Nigeria da suka tsere wa rikicin Boko Haram na fama da cututtuka a sansanonin da aka tsugunnar da su.

'Yan gudun hijirar sun ce a kowace rana suna binne yara hudu zuwa biyar wadanda ke mutuwa sakamakon wasu cututtuka da suka hada da kyanda da cutar amai da gudawa.

Haka kuma 'yan gudun hijiarar sun yi korafin cewa jami'an lafiyan da ke kula da su, sun yi karanci, lamarin daya sa ba a iya kula da rayuwar su yadda ya kamata.

Dubban mutane ne daga wasu yankuna na jihohin Borno da Adamawa ke gudun hijira zuwa wasu kasashe makwabta sakamakon hare haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa a yankin arewa maso gabashin Nigeria.