Ebola: An sake bude makarantu a Nigeria

Batun sake bude makarantu a Nigeria ya haifar da cece-kuce
Bayanan hoto,

Batun sake bude makarantu a Nigeria ya haifar da cece-kuce

An sake bude makarantu a Nigeria a hukumance bayan dogon hutun da aka karawa dalibai saboda fargabar cutar Ebola.

Daliban makarantun Firamare da na Sakandare a jihohi da dama a Nigeriar sun koma karatu a ranar Litinin.

Rahotanni sun nuna cewa galibin makarantun kudi a kasar sun dauki matakai na kariya daga cutar ebola.

Sai dai wasu jihohi a Nigeriar da suka hada da Lagos inda cutar ta soma bulla da Rivers da Kano da kuma Zamfara sun dage komawa makarantar har zuwa wata mai zuwa.

Irin wadannan jihohi sun bayyana cewa za su kara kintsawa ne sosai na daukar matakan kariya daga cutar ta Ebola.

Batun sake bude makarantun kasar ya haifar da cece-kuce a Kasar.