Coci: Mutane 115 ne suka mutu a Nigeria

Baya ga wadanda suka rasu, mutane da dama sun sami munanan raunuka a cocin dake Lagos
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta ce mutane 115 ne mafiyawancinsu 'yan Afirka ta Kudu suka mutu a lokacin da wani coci ya rushe a Nigeria.
Wani jirgin soji dauke da wadanda suka tsira da rayukansu ya sauka a birnin Pretoria kuma mutane 16 daga cikin wadanda suka tsiran sun sami munanan raunuka.
'Yan Afirka ta Kudu fiye da 300 ne suke ziyartar cocin dake Lagos, wanda fitaccen malamin addinin kiristan nan mai wa'azi a Talabijin T.B Joshua ke gudanarwa.
Sai dai hukumar bada agajin gaggawa a Nigeria ta ce mutane 86 ne suka mutu.
Ga alamu ginin cocin ya rushe ne saboda rashin kwarinsa.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti daya da BBC Safe 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 20/01/2021 wanda Sani Aliyu da Nabeela Mukhtar Uba su ka karanto.