Hari ta sama kadai ba zai murkushe IS ba

Mr. Blair ya ce Amurka da Burtaniya suna da karfin soji da ake bukata na yakar IS
Bayanan hoto,

Mr. Blair ya ce Amurka da Burtaniya suna da karfin soji da ake bukata na yakar IS

Tsohon Firaministan Burtaniya, Tony Blair ya ce bai kamata a kore batun tura dakarun yaki na kasa domin su taimaka wajen yakar 'yan kungiyar IS ba.

A wata hira da yayi da BBC, Mr Blair ya ce luguden wuta ta sama zai iya rage karfin 'ya'yan kungiyar ne kadai, amma ba zai sa ayi galaba akan su ba, a don haka, ya ce ana bukatar dakaru na kasa.

Mr. Blair ya ce akwai bukatar a samu karin dakaru na kasa daga kasashen yankin gabas ta tsakiya, inda ya ce Amurka da Burtaniya suna da karfin sojin da ake bukata.

A ranar Asabar data gabata, Shugaba Obama ya nanata alwashin da ya yi cewa Amurka ba zata tura sojojin ta na kasa ba don su yaki mayakan kungiyar ta IS.