Turkiya ta koka da yawan yan gudun hijira

Sojojin Kurdawa wadanda ke kare garin Kobani na Syria dake kusa da kan iyakar kasar Turkiya sun ce mayakan kasar musulunci suna amfani da makamai masu linzami wajen kai musu hari daga tazarar kilomita goma zuwa sha biyar.

A waje guda kuma gwamnatin Turkiya ta ce yawan Kurdawan Syria dake gujewa dannawar mayakan kasar musuluncin suna karuwa matuka.

Mataimakin Firaministan Turkiya Numan Kurtulmus yace kasarsa na shirin tunkarar abin da ya kira yanayi mawuyaci na kwararar dubban yan gudun hijira.

Yace yanzu idan harin mayakan IS ya cigaba a garin Kobani, kamar yadda aka sani akwai birnin dake dab da kan iyakar kasar mu, saboda haka akwai yiwuwar mutanen wadannan garuruwa su kwararo zuwa cikin Turkiya da yawan gaske.