An hana shugaban Uganda sauka a Otel

Shugaban Uganda Musevini
Bayanan hoto,

Shugaban Uganda Musevini

Wasu otel-otel na birnin Texas da ke Amurka sun ki saukar shugaban kasar Uganda a Otel dinsu saboda adawar da yake yi da auren jinsi daya.

Mai magana da yawun shugaban kasar Sarah Kagingo ta ce a yanzu shugaban kasar ta Uganda ya sauka ne a wani gidan gona da ke Texas.

Ta kuma kara da cewa otel-otel din sun dauki matakin kin saukar shugaban ne bayan sun fuskanci matsin lamba daga kungiyoyi masu goyon bayan luwadi da madigo.

Shugaban na Uganda ya je Texas ne domin taron zuba jari, kafin daga bisani ya wuce New York domin taron babban zauren majalisar dinkin duniya.