Kasashen Larabawa sun shiga yaki da IS

An soma kaddamar da hare hare akan mayakan IS
Bayanan hoto,

An soma kaddamar da hare hare akan mayakan IS

Jami'an Amurka sun ce Saudi Arabia da Daular Larabawa da Jordan da Bahrain da Qatar sun kasance cikin hare- haren da ake kaiwa a Syria kodayake basu ce ga matsayinsu ba.

Jordan ta fitar da wata sanarwa tana mai cewa ta tura jirginta a hare haren da ake kaiwa mayakan Islamar domin tabbatar da zaman lafiya da kuma tsaron iyakokinta da kuma dakile shigowar masu gwagwarmaya da makaman.

Shugaban gamayyar 'yan adawar Syria Hadi al-Bahra ya ce kasashen duniya sun hade dasu a yanzu, a yakin da suke yi da Kungiyar IS.

Amma ya yi kira da a kara matsin lamba akan gwamnatin Syria.