An yankewa surukin Bin- Laden hukunci

An yankewa surukin tsohon shugaban kungiyar al-Qaeda Osama bin- Laden hukuncin daurin rai da rai a wani gidan kurkuku a New York bayan an same shi da laifin ta'addanci.

A watan Maris, wasu masu taimakawa Alkali yanke hukunci a New York suka same Suleiman Abu Ghaith da laifin hada baki domin kashe Amurkawa da kuma samar da kayayyakin taimakawa 'yan ta'adda.

Alkalin, Lewis Kaplan ya fadawa Sulaiman Abu Ghaith cewa ya yi kama da wanda yake son ganin ya yi duk wani abu da zai iya yi domin kaddamar da ajandodin al-Qaeda.