China na kera abubuwan azabtarwa

Kasashen Afirka na mu'amala da kamfanonin China masu kera kayayyakin azabtarwa
Bayanan hoto,

Kasashen Afirka na mu'amala da kamfanonin China masu kera kayayyakin azabtarwa

Wasu daga cikin irin wadannan kayayyaki da kamfanonin Kasar China ke kerawa sun hada da hayaki mai sa kwalla da harsashen roba da motocin kwantar da tarzoma wadanda suke da babban hadari wajen keta hakkin bil'adama.

Ire iren wadannan kamfanoni masu kera irin wadannan miyagun na'urori na kuntawawa jama'a na kara yin yawa a China.

A shekarar 2012 daya daga cikin irin wadannan kamfanoni mai suna Xinxing ya yi mu'amalar ciniki da Kasashen Afirka sama da guda 40 tare da yin ciniki na sama da $100m na irin wadannan kayayyaki masu hadari.

Kungiyar Amnesty International ta gano cewa yanzu haka sandunan da jami'an tsaro ke amfani da su a Kasashen Ghana da Senegal da Masar da kuma Madagascar an kerasu ne a China.