An rufe iyakokin Saliyo saboda Ebola

Yaki da cutar Ebola
Bayanan hoto,

Yaki da cutar Ebola

Wani kakakin rundunar soji a Saliyo ya ce an rufe dukkanin iyakoki tsakanin Liberia da kasar Guinea a wani mataki na dakile yaduwar ebola.

An jibge sojoji a dukkan wata mashiga dake kan iyakokin.

Tun farko shugaban kasar Saliyon Ernest Bai Koroma ya ce kasarsa na nazarin sake sanya wata dokar hana shiga da fita domin dakile yaduwar kwayar cutar a fadin kasar.

Cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Amurka ta yi gargadin cewa idan lamarin ya yi kamari, mutane fiye da miliyan daya a yammacin Afirka ka iya kamuwa da cutar.

Sai dai cibiyar ta ce gangamin kasashen duniya na iya taimakawa wajen rage yaduwar cutar.