Tarayyar turai ta gargadi Google

Ana zargin Google da wuce wuri a nahiyar turai
Bayanan hoto,

Ana zargin Google da wuce wuri a nahiyar turai

Tarayyar turai ta ce kamfanin Google zai iya fuskantar tuhuma matukar ya kasa fitar da shirin da zai ba da muhimmanci ga sauran kamfanoni samar da hanyoyin neman bayanai da ke gogayya da shi.

Kawo yanzu dai an yi yunkuri har sau uku don ganin an kawo karshen wannan takaddama da aka dauki dogon lokaci ana yi.

Kwamishina mai kula da gasa Joaquin Almunia ya shaidawa wani kwamitin Majalisun dokoki tarayyar turai cewa matakin da za a dauka anan gaba, shi ne fitar da sanarwa kin amincewa da kuma takardar tuhuma.

Kamfanin Google dai ya ce zai ci gaba da aiki da tarayyar turai.

Ana zargin kamfanin ne da wuce matsayin sa a nahiyar turai inda ake da kusan kashi 90 na maso alaka da hanyoyin neman bayanai na kamfanin.

Tun a shekarar 2010 ne ake takaddama lokacin da sauran kamfanonin da ke gogayya da Google da suka hada da Foundem suka yi korafi kan yadda kamfanin ke bayyana sakamakon neman bayanai.