'Yan bangar Internet a Nigeria

Bangar siyasa harka ce data dabaibaye mafi yawancin zabubbukan da aka gudanar a Nigeria a shekarun baya.

'Yan siyasa na amfani da tarin miliyoyin matasa marasa aikin yi wajen cimma burinsu na siyasa.

Ana horar da wadannan matasa da kuma basu kudade domin yin magudin zabe.

Aikinsu shi ne duk wani abu da ya kama daga yiwa abokan hamayyar siyasa barazana zuwa kwace akwatunan zabe da kuma lakadawa jami'an zaben da basa bada hadin-kai duka.

Amma sai dai lokaci na canzawa

A madadin samar musu da makamai, a yanzu 'yan siyasar Nigeria na baiwa irin wadannan matasa kwomfitoci da wayoyi komai da ruwanka da kuma hanyoyin shiga internet

Bangar siyasa ta koma Intanet

Yayinda Nigeria take shirin tunkarar zaben shekarar 2015, ana daukar gungun matasa a daukacin Kasar domin yin amfani da internet wajen tozartawa da kuma yiwa abokan hamayyar siyasa barazana ko kuma wadanda ke da ra'ayoyi da ya sha banban da nasu.

Ga matasan Nigeria da dama, kasancewa 'dan bangar internet' wani cikakken aiki ne.

Wasu kan yi aiki daga gida, wasu kuma daga ofis, da dama na aiki dare da rana.

Wani matashi mai shekaru 28 da haihuwa da ya kammala karatunsa na digiri na daga cikin 'yan bangar Internet da ke yiwa wani fitaccen dan siyasar Nigeria aiki.

Ya kan shirya a kowacce safiya ya tafi ofis inda zai taradda tarin matasa da suke da manufa irin tasa.

Ya ce 'nakan yi amfani da batun cin hanci da rashawa da kuma kabilanci wajen muzanta wani dan siyasa'.

Ba karairaya kasusuwa

Wani matashi ya bayyana cewa wasu kafofin Internet musamman jaridu na toshe duk wani tsokaci da mambobin kungiyarsu ke sanyawa domin goyawa dan takarar su baya.

Wasu kuwa suna bada damar goyawa dan takararsa baya, su kuma ki baiwa abokan gaba damar yin tsokacinsu.

Zabubbukan dake tafe a Nigeria na cike da abubuwa na mamaki, musamman ga wadanda suka dogara da Internet wajen auna yadda 'yan Nigeria ke kallon batutuwa da dama.

A waje guda kuma 'yan Nigeriar da suke fita cikin ruwan sama ko kuma karkashin zafin rana, suna share sa'oi da dama domin su kada kuri'a a ranar zabe, yawancinsu ba su da layukan intanet

Ana amfani da kwakwalwa a madadin karfi yanzu. Babu karya kasusuwa, babu fasa baki, babu zubarda jini, ba bu asarar rayuka

Alkawuran da aka karya

Shin menene zai kasance ga irin wadannan matasa da ake dauka irin wannan aiki idan har ba a sami nasarar yakin neman zaben shekarar 2015 din ba, ko kuma aka sami nasara.

Duk da alkawuran da maiyiwuwa aka yi musu, sai dai ba dukkanninsu ne za a baiwa ayyuka ko wani matsayi a gwamnati ba.

Masu gwagwarmaya da makamai a Niger Delta wadanda suka addabi yankin kudancin Nigeria wasu 'yan shekaru da suka gabata, an ruwaito cewa an yi amfani da su a matsayin 'yan banga a lokacin yakin neman zabe wadanda kuma daga baya suka nemarwa kansu ayyukan yi.

Amma sai dai suna da isassun makamai a hannunsu bayan kammala zabe.

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram da a yanzu ke addabar arewacin Nigeria, su ma sun samu ne sakamakon irin wannan yanayi.

Ana alakanta karuwar ayyukan fashi da makami da sace- sace da kashe- kashen dake faruwa a sassa daban- daban na Nigeria bayan zabe da matasan dake da makamai a hannunsu, wadanda kuma suka sami hanyar da zasu yi amfani da su.

Abin tambaya anan shi ne ko mai irin wadannan 'yan bangar Internet zasu yi da irin kwamfitoci da kuma wayoyin da aka basu bayan zabe?