'Muna so a binciki kudaden sayen makamai'

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun kama 'yan Najeriya biyu da wani Bayahude da aze zargin sun shigar da kudin a jirgin
Bayanan hoto,

Hukumomi a Afrika ta Kudu sun kama 'yan Najeriya biyu da wani Bayahude da aze zargin sun shigar da kudin a jirgin

Kungiyar Izalatul Bidi'a Wa'ikamatus- Sunnah a Nigeria ta bukaci a yi bincike a kan batun kama wani jirgin sama da makudan kudade a kasar Afrika ta Kudu.

Kungiyar ta kuma bukaci Majalisar dokokin da ta nema ta yi binciken $9.3 da aka kama na sayen makamai, ta fito karara ta bayyana wa 'yan Nigeria sakamakon binciken.

Ita ma kungiyar lauyoyin da ke yaki da cin hanci ta rashawa a jihar Lagos ta ce tana goyan bayan umurnin da wata Kotun Afrika ta Kudun ta bayar na kwace kudaden.

Kuma ta yi zargin cewa an fitar da kudaden ne da wata mummunar aniya, a don haka ta ce za ta kai batun gaban Kotun duniya ta ICC, don tabbatar don a hukunta duk wani mai hannu a a'lamarin.

A farkon watan nan ne aka kama jirgin saman mallakar Shugaban Kungiyar Kiristoci na Nigeria, Fasto Ayo Oritsejafor dauke da kudaden da aka shirya sayen makamai da su a kasar Afrika ta Kudu.