Liberia zata daina sare dazuka saboda agaji

Liberia za ta zama kasar Afirka ta farko da za ta dakatar da sare dazuka domin samun taimako na gudunmawar raya kasa.

Norway za ta baiwa kasar ta yammacin Afirka dala miliyan 150 domin ta dakatar da sare itatuwanta nan da shekarar 2020.

A karkashin yarjejeniyar Norway za ta taimakawa Liberia inganta sa ido da kuma kare dazukan.

Wasu manazarta sun danganta barkewar cutar ebola da sare dazuka lamarin da ya sanya jama'a cudanya da muhallin da kwayar cutar ke yaduwa.