Rikici a majalisa kan kudaden makamai

Jirgin da aka kama dauke da makuden kudade a Afirka ta Kudu na cigaba da janyo cece-kuce a Nigeria
Bayanan hoto,

Jirgin da aka kama dauke da makuden kudade a Afirka ta Kudu na cigaba da janyo cece-kuce a Nigeria

Wasu 'yan majalisar wakilan Nigeria fiye da 50 sun fice a fusace daga zauren majalisar a ranar Talata bayan da mataimakin kakakin majalisar ya hana yin muhawara kan jirgin Nigeria da aka kama makare da kudade na sayen makamai a Afrika ta kudu.

Mukaddashin kakakin majalisar Emeka Ihedioha dai ya yi watsi da shawarar wani dan majalisar ne ta yin muhawara kan wannan batu.

Hujjar da mataimakin kakakin majalisar ya gabatar ita ce batu ne da ya shafi tsaron kasa.

Sai dai 'yan majalisar da suka fice daga zauren majalisar sun yi zargin cewa an bai wa wasu takwarorinsu toshiyar baki ta dala dubu ashirin kowanne saboda wannan batu.

Sai dai wadanda ake zargin sun musanta karbar toshiyar bakin.

Batun jirgin da aka kama mallakar Shugaban Kungiyar Kiristocin Nigeria CAN Ayo Oritsejafor makare da kudade na sayen makamai a Afirka ta kudu dai na cigaba da janyo cece-kuce a Nigeria.