Makamai: Cocin Katolika ta nisanta kanta

Shugabannin darikar katolikan sun bukaci da a hukunta duk wanda aka samu da laifi.
Bayanan hoto,

Shugabannin darikar katolikan sun bukaci da a hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Kungiyar Limaman darikar Katolika ta Nigeria ta nisanta kan ta game da badakalar jirgin sama mallakin shugaban kungiyar kiristoci ta kasar da aka kama da makudan kudade a Afirka ta Kudu.

Ana dai zargin cewa an yi niyyar amfani da kudaden ne wajen sayan makamai domin shigo da su Nigeria.

Limaman na Katolikan sun ce wannan al'amari ya tayar masu da hankali kasancewar zai iya bata sunan mabiya addinin kirista a Nigeria.

Shugabannin darikar katolikan sun bukaci a gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da laifi.

Bishop-Bishop din katolikan sun kuma zargi gwamnatin Nigeria da gazawa wajen magance hare haren 'yan Boko Haram.