Yaki da IS ba na Amurka ne kadai ba

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce luguden wuta ta sama da Amurka ke jagoranta a Syria dan ba ne na nagartaccen matakin maganin yan kungiyar kasar musulunci.

Da yake tsokaci shugaba Obama yace shigar kasashe biyar na larabawa a farmakin ya nuna cewa yakin ba na Amurka ne kadai ba.

Yace zai ci gaba da hada gangamin kasashen duniya domin yakar kungiyar jihadin.

Kakakin ma'aikatar tsaron ta Pentagon Rear Admiral John Kirby yace ya yi amanna an kakkabe wasu yan ta'adda na kungiyar Khorasan masu alaka da alka'ida a wani hari na daban da aka kaddamar akansu.

Yace ga yan Khorasan wanda wani bigire ne na manyan yan alka'ida, wannan farmaki yana da nufin karya lagon dukkan wani yunkurin kai hari akan Amurka ko kuma wasu muradu na kasashen yamma."