Saliyo ta rufe iyakarta da Guinea da Liberia

Mai magana da yawun dundunar sojin Saliyo ya bayyana cewa kasar ta rufe iyakarta da Guinea da kuma Liberia.

Ya kuma ce an tura sojoji kan iyakokin a wani mataki na hana bazuwar ebola.

Hakan na zuwa yayinda wasu jami'an sojojin Burtaniya dake da kwarewa kan harkar kiwon lafiya suka isa domin aikin warkar da masu cutar ebola.

Tunda farko Shugaban Saliyo ya ce kasarsa na duba yiwuwar sake takaita zirga zirga a duk fadin kasar domin dakile bazuwar cutar ebola.