Pentagon ta ce harin sama kan ISIL yayi nasara

Amurka da Faransa sun yi ta kai hare hare da jiragen yaki kan  'yan kungiyar IS a Iraki.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Amurka da Faransa sun yi ta kai hare hare da jiragen yaki kan 'yan kungiyar IS a Iraki.

Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta ce luguden wuta ta sama da Amurka ke jagoranta a Syria dan ba ne na nagartacce kuma dorarren mataki domin maganin yan kungiyar kasar musulunci.

Da yake tsokaci shugaba Obama yace shigar kasashe biyar na larabawa a farmakin ya nuna cewa yakin ba na Amurka ne kadai ba kuma zai cigaba da hada gangamin kasashen duniya domin cigaba da yakar kungiyar jihadin.

Kakakin ma'aikatar tsaron ta Pentagon Rear Admiral John Kirby yace ya yi amanna an kakkabe wasu yan ta'adda na kungiyar Khorasan masu alaka da alka'ida a wani hari na daban da aka kaddamar a kansu

" Ya ce, ga yan Khorasan wanda wani bigire ne na manyan yan alka'ida, wannan farmaki yana da nufin karya lagon dukkan wani yunkurin kai hari akan Amurka ko kuma wasu muradu na kasashen yamma."

Amurka da kawayenta sun kaddamar da hare-hare na farko kan mayakan kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci a Syria.

Kakakin hedkwatar tsaron Rear Admiral John Koby, ya ce an yi amfani da jiragen sama na yaki da kuma harba makamai masu linzami kan mayakan kungiyar a Syria.

Kasashen larabawa da suka shiga wajen kai wannan harin sun hada da Kasar Saudiyya da hadaddiyar daular larabawa, da Jordan da Bahrain da kuma kasar Qatar, sai dai kasashen nahiyar turai ba sa ciki.

A ranar Litini ne shugaba Obama ya bada umurnin kai hare hare ta sama akan mayakan Kungiyar ta IS a Iraki.

Kasar Faransa ma ta kai hare hare ta sama kan mayakan kungiyar a Iraki a makon jiya.