Sauyin yanayi:MDD ta jinjinawa shugabanni

Asalin hoton, Getty
Banki Moon ya ce kasashen duniya za su iya tunkarar duk wani kalubale akan sauyin yanayi
Majalisar Dinkin Duniya ta ce ba'a taba samun wani lokaci ba kamar yanzu da shugabannin duniya suka hadu wuri guda don tunkarar kalubale akan sauyin yanayi.
Babban sakataren Majalisar Ban ki Moon ya bayyana haka a taro na musamman kan sauyin yanayi a New York.
Mr Banki Moon ya ce taron ya nuna cewa kasashen duniya za su iya ta shi tsaye don tunkarar duk wani kalubale akan sauyin yanayi da ke gaban su.
Masana muhalli a nahiyar Afrika sun yi kashedin cewa akwai bukatar daukar kwakkwaran matakai na magance abubuwan da ke haddasa sauyin yanayi muddin ana son rage talauci da dimbin matsalolin da kasashen ke fuskanta.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 21/01/2021, Tsawon lokaci 1,01
MINTI ƊAYA DA BBC NA YAMMA 21/01/2021