Westgate: Tamabayoyin da ke neman amsa

Shekara guda ke nan bayan harin da kungiyar mayakan Islama suka kai katafaren rukunin shaguna na westgate a Nairobi dake kasar Kenya, sai dai har ya zuwa yanzu akwai abubuwan da suka shige wa 'yan kasar duhu game da harin.

Shi ne hari mafi muni da aka kaiwa Kenya tun lokacin da Al-Qaeeda suka kaiwa ofishin jakadancin Amurka hari a shekarar 1998 inda mutane 67 suka mutu sannan fiye da 200 suka samu raunuka.

Wasu daga cikin abubuwan da suka shigewa 'yan kasar duhu sune

Ko aikin agaji ya gamu da matsala a lokacin harin?

Tun da farko 'yan sanda da mutanen gari sun yi kokarin mayar da martani kan maharan, amma sa'oi kadan gwamnati ta aike da sojoji.

Hamayya tsakanin rundunonin biyu ta soma ne a lokacin da aka kashe Komandan 'yan sanda a wata musayar wuta da sojoji suka yi.

Wannan ya fusata 'yan sanda abinda yasa suka bar wajen cikin fushi yayinda sojoji suka karbi ikon ginin rukunin shagunan

Su waye maharan kuma sun mutu?

Kungiyar Al-shabab ta Somalia mai alaka da Kungiyar Al-qaeeda ita ce ta dauki alhakin kai harin saboda kasar Kenya ta kai dakarunta Somalia don marawa gwamnatin kasar baya mai samun goyan bayan majalisar dinkin duniya.

Mai magana da yawun rundunar sojin kasar Kenya ya bayyana sunaye hudu na maharan da suka hada da Abu Baara al-sudani da Omar Nabhan da Khattab Al-Kene da kuma Umayr.

Sai dai rahotanni na bayyana cewa dukkanninsu sun fice daga kasar kafin kai harin.

Hukumar tsaro ta FBI na nazari kan gawawwakin wadanda ake zargin maharan ne.

Me ya faru game da binciken Westgate?

Shugaba Uhuru Kenyatta ya yi alkawarin kafa wata hukuma wacce zata gudanar da binciken harin da kuma duk wani akasin da aka samu daga bangaren hukumomin tsaro.

Amma har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton babu abinda ya faru.

'Mun yi alkawari, amma majalisar dokoki sun dauki aikin kuma sun yi iyakacin kokarinsu suka fito da wani rahoto da ya fito da wasu matakai na inganta tsaron kasar' in ji ministan cikin gidan Kenya Mr Ole Lenku.

Me ya faru game da kwasar ganima?

An zargi sojoji da kwasar ganima a lokacin da hoton bidiyon CCTV ya nuna sojoji suna fita da jakunkuna daga cibiyar kasuwancin.

A lokacin da 'yan kasuwar suka koma Westgate sun tarar da cewa an farfasa shagunansu.

Hotunan da aka sanya a shafin sada zumunta sun nuna cewa an balle wuraren da ake ajjiye kudi.

Gwamnati ta ce sojojin dauke da jakunkunan na taimakawa kansu ne wajen kashe kishin ruwan dake damunsu a lokacin farmakin.

A watan Oktoba an bayyana sunayen sojoji biyu da aka caje su, aka kuma daure su saboda kwasar ganima.

Me ya faru game da biyan diyya?

Gwamnatin Kenya ta dau alkawarin biyan diyya ga wadanda suka tsira da rayukansu da kuma taimakawa musu da kudaden magani.

Amma mutanen da BBC ta tuntuba sun ce babu abinda aka yi musu.

'Mun yi ta dakon jiran gwamnati ta biya mu diyya, amma ban ga komai ba har yanzu' in ji Ms Moraa.

Wani soja da ya samu rauni sakamakon wani gurneti da aka jefa masa, shi ma ya ce yana jiran diyyar.

Gurnetin ya halaka abokan aikinsa guda biyu.