Atiku ya ce zai tsaya takara a 2015

Tsohon mataimakin shugaban Nigeria, Atiku Abubakar ya bayyana aniyyarsa ta tsayawa takara a zaben shugaban kasar da za a gudanar a shekarar 2015 karkashin inuwar jam'iyyar APC.

Atiku Abubakar ya bayyana aniyar tasa ce ranar Laraba a Abuja a gaban cincirindon magoya bayan sa.

Wannan dai shi ne karo na uku da tsohon Shugaban kasar ke neman takarar shugabancin Nijeriya.

Atiku Abubakar wanda dan asalin jam'iyyar PDP ne ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC bayan da ya yi zargin cewa ba a yi masa adalci.