Algeria: Mayakan Islama sun kashe Bafaranshe

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Kungiyar mayakan Jihadin Algeria ta saki wani faifan bidiyo wanda ta ce yana nuna wani dan yawon bude idon Faransa da take rike da shi, kansa a yanke.

Kungiyar mai suna Jund al-Khalifa wacce ke da alaka da kungiyar IS, ta kama Herve Gourdel a ranar Lahadi yayin da yake tafiya a yankin Kabylie a gabashin Algeria.

Mayakan sun bukaci a kawo karshen hare- haren sama da kasar Faransa ke kaiwa mayakan IS na Iraqi.

Gwamnatin Faransa ta maida martani tana mai cewa ba zata taba mika wuya ga barazanarsu ba, kuma zata cigaba da daukar matakin sojin.