'Yan gudun hijira na bara a Maiduguri

Rikicin Boko Haram ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu a Borno
Bayanan hoto,

Rikicin Boko Haram ya tilastawa dubban mutane barin gidajensu a Borno

Rahotanni daga Maidugurin jihar Borno a Nigeria sun bayyana cewa wasu daga cikin 'yan gudun hijirar rikicin Boko Haram musamman mata da kananan yara sun fara fita yin bara, saboda halin kuncin da suka shiga.

Dubban mutane ne suka tsere wa rikicin Boko Haram daga sassa da dama na jihar ta Borno.

Wani mazaunin birnin Maiduguri ya fadawa BBC cewa 'akwai su da yawa wadanda suke cikin gari yanzu haka basu san inda zasu je su kwana ba, suna bara kan tituna kuma suna cin abinci'.

Yayinda wasu 'yan gudun hijirar ke zaune a sansanonin da gwamnati ta tanadar musu, wasu kuwa na zaune ne a gidajen 'yan uwa.

Hukumomi da sauran jama'a na cewa suna iya kokarinsu wajen taimakawa 'yan gudun hijirar.