India za ta harba tauraro duniyar Mars

Mangalyaan shi ne tauraro na farko da Indiya ta har ba duniyar Mars
Bayanan hoto,

Mangalyaan shi ne tauraro na farko da Indiya ta har ba duniyar Mars

India za ta kafa tarihi nan gaba kadan bayan ta harba tauraron dan adam duniyar Mars.

Tauraron dan adam din mai suna Mangalyaan, ya na kara kusantar duniyar ta Mars bayan yayi tafiyar watanni goma daga duniyar Earth.

A ranar Laraba, za a kunna babban injin tauraron da wasu na'urorin da suke bashi damar shawagi a sama, domin a rage masa saurin tafiya a sama.

A baya, kasahen Amurka, da Rasha da na turai ne kadai su ka yi nasarar aika tauraron dan adam din su duniyar ta Mars.

A ranar Litinin da ta gabata ne ma Amurka ta aika sabon tauraronta, Maven duniyar ta Mars.

Idan tauraron Mangalyaan na India ya samu tsayawa a duniyar ta Mars, zai rika daukan hotunan abubuwan da ke cikin duniyar, da kuma bada damar yin nazari akan su.

A 'yan makonnin da suka gabata, anyi ta fargabar ko za a iya dogaro da aikin da tauraron dan adam din na India zai yi a duniyar Mars, ganin yadda ba a taba amfani da shi ba tunda aka harba shi daga duniyar Earth a watan Disamba.

Amma fargabar ta kau a farkon wannan makon, bayan injiniyoyi sun tantance duk kan bangarorin tauraron suna aiki.

Bayanan hoto,

Tauraron Mangalyaan zai rika daukan hotunan abubuwan da ke cikin duniyar Mars

Tauraron na Mangalyaan zai yi trafiya zuwa bayan duniyar Mars, kamar yadda za a iya ganin sa daga gefen rana da kuma duniyar Earth.

Tauraron dan adam din na India, an kaddamar da shi ne daga tashar sararin samaniya ta Sriharikota a ranar 5 ga watan Nuwanban 2013.

Kudin India rupee biliyan hudu da miliyan dari biyar ne aka ware wa aiki harba tauraron duniyar Mars, dai dai da dala miliyan 74, wanda shine kudi mafi karanci da aka taba kashewa a aikin harba tauraron dan adam wata duniya.

Firaiminista Narendra Modi, lokacin da ya ziyarci tashar sararin samaniya ta Sriharikota ya ce kudaden da aka kashe a yin fim din Gravity ya fi wadanda suka ware na aikin tauraron Mangalyaan.

Amma duk da haka dai, aikin harba tauraron Mangalyaan ya sha suka a ciki da wajen India, daga wuraren wadanda suke ganin kudin da aka ware wa aikin, za su fi amfani idan aka kashe su wurin kyautata rauwar miliyoyin Indiyawa wadanda basa samun wutar lantarki da tsaftar muhalli.

Gwamnatin India a gefe daya kuma, tana ganin aikin tauraron, dama ce ta kara bunkasa al'amuran fasaha a kasar.