Taron inganta shari'a na gudana a Nijar

Image caption Karancin kudade da ma'aikata na daga cikin manyan matsalolin harkokin shari'a a kasar ta Nijar.

An shiga kwana na biyu a wani taron tattauna matsalolin bangaren shari'a a Jamhuriyar Nijar domin lalubo hanyoyin magance su.

Taron na da burin kaddamar da wani daftari ne da ya kunshi matakan kyautata yanayin shari'a a Kasar nan da shekaru 10 masu zuwa.

Taron ya biyo bayan wani babban taro ne na kasa da aka gudanar a shekarar 2013, kan matsalolin shari'a.

Wani mai fafutukar kare hakkin dan-adam da ke halartar taron na cewa karancin kudade da ma'aikata na daga cikin manyan matsalolin harkokin shari'a a kasar ta Nijar.

Ministan shari'ar Nijar ya ci alwashin cewa gwamnati za ta yi amfani da shawarwarin wannan taro wajen inganta harkokin shari'ah a kasar.