'Yan gudun hijira a Kamaru na cikin kunci

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dubban mutane ne daga wasu yankuna na jihohin Borno da Adamawa ke gudun hijira zuwa wasu kasashe makwabta

'Yan Nijeriya da suka yi gudun hijira zuwa Jamhuriyar Kamaru saboda rikicin Boko Haram sun yi barazanar komawa gida duk da hatsarin da ke tattare da haka.

Sun ce halin kunci da su ke fuskanta yanzu a sansanonin 'yan gudun hijira a garin Fotokol na Kamaru ya yi tsanani matuka don haka sun gwammace su koma gida Nijeriya.

Rahotanni sun ce a kowace rana 'yan gudun hijira biyar zuwa shida ne ke mutuwa sakamakon cututtuka da suka hada da zazzabin cizon sauro, amai da gudawa da kyanda da mura.

Dubban mutane ne daga wasu yankuna na jihohin Borno da Adamawa ke gudun hijira zuwa wasu kasashe makwabta sakamakon hare haren da 'yan kungiyar Boko Haram ke kai wa a yankin arewa maso gabashin Nigeria.