Sudan ta Kudu ta kauce wa yunwa

Sudan ta Kudu ta kauce wa yiwuwar fuskantar fari a bana, sai dai ana hasashen cewa mai yiwuwa ta fuskanci wannan matsala shekara mai zuwa.

Kwararru kan matakan wadata kasa da abinci a kasar, sun yi gargadin cewa matukar ba a dauki wasu matakai na tara kudade ba, da kuma rarraba abinci, da sauran abubuwan ci masu gina jiki, kafin karshen shekara, mutane da yawa za su kasance cikin hatsari.

Rahoton ya ce yankunan da rikici bai shafa ba sun samu wadatar abinci, sai dai akwai hasashen cewa mutane fiye da miliyan daya da rabi na cikin matsalar yunwa, adadin da ka iya ninkawa a shekara mai zuwa.

Sudan ta Kudu dai ta samu 'yancin kan ta ne daga Sudan.