Cece-kuce kan tantance lafiyar Suntai

Bangaren Gwamna Suntai ya ce kwamitin binciken haramtacce ne
Bayanan hoto,

Bangaren Gwamna Suntai ya ce kwamitin binciken haramtacce ne

A Nigeria, ana cigaba da cece-kuce a Taraba ga me da matakin da majalisar dokokin jihar ta dauka na kafa kwamiti domin tantance matsayin lafiyar gwamnan jihar Danbaba Suntai.

Kwamitin zai gudanar da bincike ne akan ko gwamna Suntai zai iya komawa kan kujerar mulki ko kuma a'a.

Sai dai a ranar Talata wata kotu ta saurari kara da wasu a bangaren gwamnan suka shigar ta neman a dakatar da aikin kwamitin,

Magoya bayan Danbaba Suntai suka ce kwamitin haramtacce ne saboda wata kotu a Jalingo ta dakatar da cigaba da bincike akan lafiyar gwamnan.

Kimanin shekaru biyu kenan da Jihar Taraba ta fada cikin rikici na siyasa tun bayan da Gwamna Danbaba Suntai ya yi hatsarin jirgin sama, lamarin da likitoci suka ce ya taba kwakwalwar sa.