Taraba: Za a tantance koshin lafiyar Suntai

Ana tababa akan koshin lafiyar Gwamna Suntai wanda ya yi hatsarin jirgi
Bayanan hoto,

Ana tababa akan koshin lafiyar Gwamna Suntai wanda ya yi hatsarin jirgi

Majalisar dokokin jihar Taraba a Nigeria ta ce babu gudu babu ja da baya a yunkurinta na tantance matsayin lafiyar Gwamnan jihar Danbaba Suntai.

Majalisar za kuma ta yanke hukunci kan ko zai iya komawa kan kujerar mulki ko kuma ba zai iya ba.

Wanan dai ya biyo bayan wani hukuncin kotu ne da ya yi watsi da bukatar bangaren Gwamna Suntai ya gabatar ta neman a dakatar da aikin wani kwamitin kwararrun masana kiwon lafiya da majalisar ta kafa domin binciken lafiyar Gwamnan.

Yanzu dai majalisar ta ce wannan hukuncin kotu ya ma kara mata kaimi a kokarin auna lafiyar Danbaba Suntai domin sani makomarsa game da Shugabancin jihar.