Boko Haram: Mutane 13,000 ne suka mutu

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigeria ta nemi kasashen duniya su bankado inda Boko Haram ke samun kudade da makamai

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan ya bayyanawa shugabannin duniya cewa rikicin Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar mutane13,000 a shekaru biyar da suka gabata.

Shugaba Jonathan ya bayyana haka ne a lokacin da yake yin jawabi ga taron kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya a birnin New York akan barazanar ta'addanci ga zaman lafiyar duniya.

Goodluck Jonathan ya ce barazanar ta'addanci a arewa maso gabashin Nigeria kalubale ne ga zaman lafiyar Kasar.

Shugaban Nigeriar ya kuma ce dole ne majalisar dinkin duniya ta nuna damuwarta game da yadda kungiyar Boko Haram take samun kudaden shiga da makamai.