An rufe makarantar Islamiyya a Kenya

Madrassa

Mahukunta a kasar Kenya sun rufe wata makarantar Islamiyya da suka ce tana koyar da tsatsaruan ra'ayi.

An kai samame makarantar da ke unguwar Machakos, a gabashin birnin Nairobi ne, bayan tsare wasu matasa da aka yi a bisa zarginsu da ake yi da shiga cikin kungiyar mayakan Al Shabab na Somalia.

Wani babban jami'in dan sanda ya ce za a sake bincikar wasu makarantun.

Mayakan Al Shabab na Somaliyar dai sun sha kai hare-hare a kasar ta Kenya.

Karin bayani