Babu batun tsawaita kwantiragi - Lampard

Frank Lampard Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Manuel Pellegrini ya ce Lampard zai iya ci gaba da zama a Man a City

Dan wasan Manchester City Frank Lampard ya ce babu wata tattaunawa da suka da kungiyar game da batun tsawaita kwantiraginsa.

Dan shekaru 36, Lampard, ya zira kwallaye uku a wasannin uku ne kawai tun bayan da ya koma City.

A watan Janairu mai zuwa kwantiraginsa zai kawo karshe, ko da yake mai horar da 'yan wasan Manuel Pellegrini ya ce zai iya ci gaba da zama a kungiyar.

"Ina nan har na da zuwa watan Janairu, abinda kawai zan iya fada ke nan." In ji Lampard.