Za a daina sayar da komfutar Samsung

Hakkin mallakar hoto samsung
Image caption Kamfanin Samsung ya ce yana la'akari da yanayin kasuwa

Kamfanin Samsung ya ce zai daina sayar da komfutarsa ta tafi da gidanka a nahiyar turai.

Wannan yunkuri ya hada har da samfurin Chromebook wanda a baya ya kasance samfurin da aka fi saye tsakanin komfutoci irin sa.

Shawarar da kamfanin Samsung na kasar Koriya ta Kudu ya dauka ta biyo bayan sanarwar da kamfanin Sony ya fitar a farkon wannan shekarar cewa zai sayar da sashen Vaio tare da janyewa daga sayar da komfutar tafi da gidanka baki daya.

Sai dai a 'yan kwanakin nan wasu kamfanoni sun sanar da samun bunkasa a bangaren.

Haka kuma akwai alamun cewa mai yiwuwa kamfanin Samsung ya dauki irin wannan mataki a sauran sassa na duniya.

A wata sanarwa Samsung ya ce " mu na la'akari ne da yanayin kasuwa da kuma bukatun al'umma".

A bangare guda kuma kasuwar manyan wayoyin tafi da gidanki na Samsung din ta ragu a 'yan watannin nan.

Bincike ya nuna cewa wayoyin Micromax da Xiaomi a India da China sun karbe kasuwar wayoyin tafi da gidanka na Samsung.