Boko Haram: Nigeria za ta karbo bashi

Hakkin mallakar hoto
Image caption An yi ta cece kuce a Nigeria kan bukatar karbo bashin

Majalisar dattawan Nigeria ta amince da bukatar Shugaban kasa ta karbo bashin $1 biliyan domin yaki da masu tayar da kayar baya.

Shugaba Jonathan ya rubutawa majalisar dattawan Kasar wasika a ranar 15 ga watan Yuli yana neman ta amince da bukatar karbo bashin

Majalisar ta amince da wannan bukata ne bayan da wasu kwamitocin hadin-gwiwar majalisar biyu, da suka hada da na harkokin kudi da basussukan cikin gida dana waje suka duba batun kuma suka mika rahotan su ga zauren majalisar ranar Laraba

Rahotan kwamitocin biyu dai ya ce za a yi amfani da kudaden da za a karbo bashin ne domin sayo sabbin kayan yaki, don kawo karshen hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram.