Kamaru: Mun kama wani jagoran Boko Haram

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rikicin Boko Haram na shafar rayuwar dumbin mutane a yankunan da ke tsakanin Nigeria da Kamaru

Hukumomi a Jamhuriyar Kamaru sun ce sun kama wani shugaban kungiyar Boko Haram, da ake kira Abakar Ali.

Jami'ai sun ce sun kama Abakar Ali, da ke jagorantar reshen kungiyar Boko Haram ne a garin Kousseri na arewacin kasar a wani samamen jami'an tsaro.

Haka zalika, sun ce sun kama wasu mutane biyu da suke abokan aikinsa, sun kuma gano wata maboyar makamai.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da matsayin mutanen da ke tsare.

A baya dai, Nigeria dai na zargin makwabciyarta Kamaru da kin tashi tsaye wajen dakile ayyukan mayakan Boko Haram wadanda sau tari suke shawagi tsakanin kan iyakar kasashen.