Amurka ta ce babu tabbas mutuwar Shekau

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An sha yin shelar kashe Abubakar Shekau a Nigeria amma daga bisani ya sake bayyana

Gwamnatin Amurka ta ce har yanzu ba ta samu wata shaida da za ta tabbatar da ikirarin gwamnatin Nigeria ba, na mutuwar Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Wani jami'in harkokin wajen Amurka, Rodney D Ford ya ce suna ci gaba da kokarin tabbatar da sahihancin ikirarin gwamnatin Nigeria, da gaskiyar cewa akwai mutanen da ke shigar-burtu da sunan Abubakar Shekau.

A baya dai, rundunar tsaron Nigeria ta ce dakarunta sun kashe wani mutum da ke batar da kama da sunan shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau yayin fafatawa a garin Kunduga.

Mai magana da yawun shalkwatar tsaron Nigeria, Manjo Janar Chris Olukolade ya yi ikirarin cewa Abubakar Shekau ya jima da mutuwa amma wasu ke yin shigar-burtu don ci gaba da yada angizon kungiyar.

Babu wata kafa mai zaman kanta da ta tabbatar da batun mutuwar Abubakar Shekau jagoran kungiyar Boko Haram.