Ebola: mutane sama da 3,000 sun mutu

 Ebola
Image caption Mutane 150 sun mutu a Liberiya cikin kwanaki biyu

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce mutane sama da dubu 3000 ne suka mutu daga cutar Ebola a Yammacin Afrika, cikin mutane kusan mutane 6,500 da suka kamu da cutar.

Kasar Liberiya ce dai lamarin ya fi kamari, a cewar hukumar, inda mutane akalla 150 suka mutu cikin kwanaki biyu.

Hukumar ta WHO ta kara da cewa akwai yuwuwar mutanen da suka mutu cikin kwanakin biyun sun fi haka domin wasu da dama na tsoron su tunkari asibiti.

Wakilin BBC a yankin ya ce yanzu adadin mutanen da ke mutuwa daga cutar ta Ebola a kasar ta Liberiya, ya dara na ko ina.

Tuni dai Hukumar ba da lamuni ta duniya, IMF ta yi alkawarin bayar da tallafin dala miliyan 30 ga kasashen Liberiya da Guinea da kuma Saliy dom,in yaki da cutar ta Ebola mai saurin hallaka mutane.