Fifa ka iya haramta mallakar hadin gwiwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An ce jami'an Fifa da dama na cewa su ba su ga wata illa ga kyautar agogunan ba

Ana sa ran Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa za ta fitar da wata muhimmiyar sanarwa game da tsarin mallakar hadin gwiwa da Kamfanonin zuba jari ke yi a kan 'yan wasan kulobluka.

Dokokin gasar Firimiyar Ingila sun haramta tsarin, wanda ya zama ruwan dare a nahiyar Turai da Amurka ta kudu, inda Kamfanoni ke neman riba a kan hannun jarinsu a kan 'yan wasa.

Dan wasan Manchester City, Eliaquim Mangala da aka saya a kan fam miliyan 32 daga Porto, daya ne daga cikin manyan yarjeniyoyi hudu da aka kulla bana ta hanyar tsarin mallakar hadin gwiwa.

Sashen wasannin BBC ya fahimci cewa Fifa ta tattauna kan wannan batu ranar Alhamis, a taron kwamitin zartarwarta a Zurich din Switzerland.

Haka zalika, an yi imani cewa a farkon wannan mako, kwamitin tantance matsayin 'yan wasa na Fifa, da ke kula da batun musayar 'yan wasa ya kada kuri'ar ba da shawara don haramta tsarin mallakar 'yan wasa na hadin gwiwa.

Tattaunawar ta biyo bayan matsin lambar da ake samu daga Uefa, da ke son bullo da sabbin dokoki don hana tsarin mallakar 'yan wasa na hadin gwiwa.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Shawarar haramta tsarin ka iya yin matukar tasiri a kan gasar kwallon kasashe da dama, inda suka dogara sosai a kan wannan tsari, da kuma kungiyoyin kwallon kafa da suka dogara a kan masu zuba jari wajen mallakar 'yan wasa.

Haka zalika, sashen wasannin BBC ya fahimci cewa jami'an kwamitin zartarwar Fifa da dama ba sa farin ciki a kan matakin da kwamitin da'a ya dauka a kan agogunan Parmigiani na fam dubu 16 da suka karba daga Hukumar kwallon kafa ta Brazil a lokacin gasar cin kofin duniya.

An bai wa jami'an zuwan nan da karshen watan gobe su mayar da agogunan ko kuma su fuskanci ladabtarwa saboda darajar agogunan ta zarce ka'idar Hukumar Fifa.