Zawarawa a Indiya na gudanar da bore

Image caption Wani mai fafutukar kare hakkin mata ya ce ana kallon zawarawa a Indiya kamar wasu miyagun mutane

Wasu zawarawa a Indiya sun koma gida birnin Kolkata a yammacin Bengal don nuna adawa a kan mawuyacin halin da matan da ake kora bayan mutuwar mazajensu ke ciki

Mata na shiga halin kunci bayan danginsu sun kore su daga gidajen mazajensu da suka mutu.

Ana fada wa dubban zawarawa a Indiya cewa sun zama nauyi, ko kuma suna kai wa danginsu rashin nasara.

Akwai zawarawa kimanin dubu 20 a arewacin birnin Vrindavan, inda damansu ake tilas wa yin bara a tituna.

Ayarin zawarawan da ya koma Kolkata za su bukaci gwamnan jihar West Bengal ya kara jajircewa wajen taimaka musu.