Musulmai sun yi tir da fille kan Bafaranshe

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyoyin 'yan gwagwarmaya musammam ma daular musulunci na fille wuyan 'yan kasashen yamma a baya-bayan nan

Dubban Musulmi ne suka taru a garuruwa da biranen Faransa don yin tir da masu ikirarin jihadi a kasar Aljeriya a kan kashe wani Bafaranshe dan yawon shakatawa.

'Yan tada-kayar-baya masu alaka da kungiyar daular musulunci sun fitar da wani hoton bidiyo da ke nuna fille wuyan Herve Gourdel.

Daraktan Babban Masallacin birnin Paris kuma babban malamin addinin musulunci a Faransa, Dalil Boubakeur ya fada wa taron musulmin cewa kisan gillar aikin ragwaye ne.

Ya kalubalanci yadda mutanen da suka yi dumu-dumu cikin abun da ya kira ta'addanci ido rufe da dabbanci ke amsa sunan musulmi.

Daruruwan mutane ne a taron wanda Magajin garin Paris ya halarta suka tafa wa wannan tsokaci.