Amfani da wayoyin salula a jiragen sama

Jiragen Air France Hakkin mallakar hoto Reuters

Hukumomin zirga-zirgar jiragen sama a Nahiyar Turai sun ce a yanzu fasinjoji za su iya amfani da wayoyinsu na salula a lokacin da jirgin sama ya tashi.

Wannan sanarwar ta bayar da dama ga fasinjoji su shiga shafukan intanet a wayoyinsu na salula da naurorin Tablet na hannu don aikewa da sakon imel a lokacin da jirgi ke tafiya a nisan mita 3,000 a sararin samaniya.

Sai dai bayanai sun nuna cewa ba za'a iya kiran waya a irin wannan yanayi ba sai idan an sanya wa jirgin wata naura ta musamman da za ta bayar da damar yin kira.

A baya dai Nahiyar Turai na bayar da dama ne mutane su yi amfani da wayoyinsu na salula a cikin jirgi idan sun sanya wayar a tsarin tafiya a jirgi, don kaucewa haddasa matsala ga matuka jirage.

Karin bayani