An killace jami'ar lafiya a Liberia

Hakkin mallakar hoto AFP

Babbar jami'ar da ke kula da kiwon lafiya a kasar Liberia ta kebe kanta domin a sa-mata-ido game da cutar Ebola, sakamakon mutuwar da wani makarrabinta ya yi daga cutar.

Jami'ar, wadda ita ce mataimakiyar ministan lafiya, ta ce za ta kasance a gida har na tsawon kwana 21.

Ta shaida wa BBC cewa tana so ne ta kasance abin misali wajen bin dokar, wadda tace da ita aka kafa ta.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutane 3000 ne suka mutu daga cutar Ebolan a shiyyar Afirka ta Yamma.

Kasar Liberia ce cutar tafi yi wa barna, inda Hukumar Lafiya ta Duniya tace akalla mutane 150 sun mutu a cikin kwanaki biyu kacal.

Karin bayani