Hajj: An fara jigilar alhazai daga Enugu

Hajj Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan shine karon farko da aka fara jigilar alhazai daga Enugu

A karon farko, maniyyata aikin Hajjin bana daga wasu jihohi uku na shiyyar kudu maso gabashin Najeriya, sun tashi zuwa Saudi Arabia daga babban filin jirgin sama na Akanu Ibiyam da ke birnin Enugu.

A shekarun baya ana jigilar alhazan wannan siyyar ne daga garin Fatakwal.

Ko da yake an gamu da wasu 'yan matsaloli, amma akasarin maniyyatan sun bayyana farin cikinsu game da wannan sabon shiri.

Ana su bangaren kuma hukumomin alhazai sun ce su ma sun farga da matsalolin da aka fuskanta, kuma suna fatan za a warware su nan gaba.

Akalla maniyyata 280 daga jihohin Abia da Anambra da Ebonyi aka yi jigilarsu zuwa kasar Saudia daga Enugun.