Amurka ta kai wa IS hari a Kobane

Jiragen yaki Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jiragen yaki

An ba da rahoton wasu hare-hare ta sama da aka kai kan wasu wurare a garin Kobane da ke arewacin Syria, a daidai lokacin da Amurka da kawayenta ke zafafa yakin da take yi da 'yan kungiyar masu jihadi.

Ana jin karan jiragen yaki na shawagi a saman garin ba kakkautawa, yayin da a bangare guda kuma, mayakan Kurdawa da ke Syria ke dagewa wajen kare garin Kobanen daga 'yan kungiyar masu jihadin ta kasa.

Rahotanni sun ce lokuta kalilan ne su ka rage a fatattaki masu jihadin daga gain na Kobane.

A jawabin da yakan yi na mako-mako, shugaban Amurka Barak Obama ya ce Amurka na jagorantar yakin ne da nufin murkushe 'yan kungiyar masu jihadi.

A bangare guda kuma jiragen yakin Birtaniya sun fara aikin su na farko a Iraqi tun bayan lokacin da majalisar dokokin kasar ta basu izinin kai hari ta sama kan kungiyar masu jihadin.

Jiragen yakin dai makare suke da kayayyakin da suka hada da bama-bamai da kuma makamai masu linzami.

Tun da farko an shirya cewa jiragen yakin Birtaniya za su kai hari ne akan masu jihadin da ke Iraqi, amma Firaminista David Cameron ya nuna cewa yakamata a fadada matakin zuwa

Karin bayani

Shafuka masu alaka

BBC ba tada alhaki game da shafukan da ba nata ba