Manyan 'yan takara 3 na jam'iyyar APC

Image caption Jama'a sun sa ido domin ganin wanda jam'iyar APC za ta tsayar takara

A Nigeria, hankulan wasu 'yan kasar da masu lura da al'amura a yanzu sun karkata ne ga jam'iyyar hamayya ta APC don ganin yadda za ta kaya wajen fidda mutumin da zai yi mata takarar shugabancin kasa a zaben badi.

Kawo yanzu dai mutane uku ne suka nuna aniyar yin takarar shugabancin a jam'iyyar da suka hada da tsohon shugaban mulkin sojan kasar, Janar Muhammadu Buhari.

Sauran sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasar Alhaji Atiku Abubakar, da kuma Gwamnan Kano mai ci Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Wasu masu sharhi dai na cewa jam'iyyar za ta iya fuskantar kalubale mafi girma tun bayan kafuwar ta, idan aka zo fidda gwanin.

To sai dai duka bangarorin masu neman takarar na cewa ba su dauki lamarin da zafi ba.