Talauci da fatara ke sa mutane barin kasashensu

Wasu 'yan cirani da suka muta a Nijar Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wasu 'yan cirani da suka muta a Nijar

A jamhuriyar Nijar, hukumar yaki da masu safarar mutane ta kasar ta shirya wata mahawara domin fadakar da mutane akan matsala da illlolin da ke tattare da safarar mutane.

A jiya ne dai aka gudanar da bikin yaki da safarar mutane a kasar,da ake yi a ranar 28 ga watan satumba na kowace shekara,

sai dai yayin da wasu ke ganin talauci da fatara ne ke sa wasu 'yan Nijar tafiya kasashen waje, inda suke yin wasu ayyuka da wasu ke ganin na cin zarafi ne domin samun abin rufin asiri,wasu na cewa ba haka maganar take ba.

Sai dai wasu na ganin zamantakewar mutane ita ce ya kamata a sauyata yadda maza zasu rika kula da iyalansu yadda ya kamata.

A bara ne ankagano gawawwakin mata da yara kanana su 92 da suka fito daga yankin Damagram da suku mutu sakamakon kishin ruwa da yunwa lokacinda da suke kokarin tsallkawa zuwa kasar Algeria.