An kashe mutane 6 a Taraba

Hakkin mallakar hoto AP

Rahotanni daga jihar Taraba a Najeriya sun ce akalla mutane shidda sun rasa rayukansu a wani hari da aka kai masu yayin da suke komawa gida daga kasuwa.

Lamarin ya faru ne tsakanin kauyen Unguwar-Kwalla da garin Dampar a karamar hukumar Ibi, inda aka yi wa matafiyan kwanton bauna.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da faruwar lamarin amma ta ce mutum daya ne aka kashe.

Rahotanni dai sun nuna cewa 'yan bindiga ne suka tare wasu mutane da suka fito daga wata kasuwar da ke ci a ranar Asabar a kauyen Unguwar Kwallan.

Bayanai sun ce mutanen 'yan garin Dampar ne, kuma wani mazaunin garin, Sadanu Isa Tukari, wanda ya ce ya na cikin wadanda suka kwashi gawawwakin mutane shiddan da aka kashe, ya ce harin na da dangataka da kabilanci.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Taraba, DSP Joseph Kwaji, ya tabbatar da cewa an kai harin, amma ya ce 'yan fashi ne suka kai shi.

Ya kuma ce mutum daya ne kawai aka kashe, aka kuma jima wasu raunuka.

Karin bayani