Afghanistan: Kalubalen dake gaban Shugaba Ghani

Hakkin mallakar hoto Reuters

Bayan dogon lokacin da aka dauka ana rikicin zabe a yanzu da Afghanistan ta samu sabon Shugaba, Ashraf Ghani ba zai yi wata wata ba wajen soma aiki gadan- gadan

An rantsar da shi ne bayan wata da watannin da aka shafe cikin halin rashin tabbas, yayinda zarge- zargen tafka magudi a zaben shugaban Kasar ya sa tilas aka sake kirga dukkanin kuri'un da aka kada.

Sai dai Amurka ta shiga tsakani wajen ganin an kafa gwamnatin hadin kan kasa

Manyan kalubalen dake gabansa guda biyar

Hada kan gwamnati

Wata yarjejeniyar raba madafan iko ce ta baiwa abokin hamayyar Mr. Ghani, Abdullah Abdullah wani mukami kwatankwacin na Firai Minista

Duk da cewa dukkanin mutanen biyu sun goyi bayan yarjejeniyar da Amurkar ta kulla a bainar jama'a , sai dai har yanzu wasu na kut da kut da Mr. Abdullah sun fito karara suna nuna cewa akwai sauran rina a kaba.

Sun yi imanin cewa an yi magudi a nasarar da Mr. Ghani ya samu

Saboda haka a jerin manyan abubuwan da sabon Shugaban zai yi shi ne yadda zai hada kan sabuwar gwamnatin da aka kafa da kuma karfafa ta

Dole ne gwamnatin ta kawo sauyi a tsarin zaben kasar cikin gaggawa da kuma cikin lokaci saboda zaben majalisar dokokin dake tafe shekara mai zuwa.

Wannan ba abu bane mai sauki, kuma 'yan Afghanistan da dama na da damuwar cewa wannan yarjejeniyar gwamnatin hadin kan kasar ba za ta je ko'ina ba.

Sanya Afghanistan komawa kan turbar aiki

Sanya Afghanistan komawa kan turbar aiki da kuma tabbatar da kyakkyawan yanayi na aikin na da mahimmanci.

Watanni shidan da aka shafe cikin halin rashin tabbas game da sakamakon zabe ya yi mummunan tasiri akan tattalin arzikin kasar, wanda dama can yake da rauni, wanda kuma ke dogaro akan tallafin kasashen waje.

A matsayinsa na masanin tattalin arzikin babban bankin duniya, wanda ya kware wajen dakile matsalar gwamnatocin da suka nuna gazawa , babu shakka Mr Ghani yana da cancanta sosai wajen aikin farfado da tattalin arzikin kasar.

Amma babbar matsalar da zai fuskanta ita ce cin hanci da rashawar da ya yi wa kasar katutu

Kodayake Mr Ghani ya ce ba zai lamince da cin hanci da rashawar ba, duk wata nasara da za a samu zata dogara ne akan ko zai iya gudanar da wani sauyi mai mahimmanci ko kuma a'a

Wanda ya gada Hamid Karzai a nan, ya kasa

Hakkin mallakar hoto Reuters

Samar da jama'a tsaro

Sojojin Afghanistan na fuskantar 'yan kungiyar Taliban da kansu

Lokacin yana da hatsari. Ashraf Ghani ya karbi mulki ne gabanin janyewar dakarun kassahen duniya zuwa karshen shekarar 2014.

Daga shekara mai zuwa ne, dakarun kasar marasa kayan yaki na zamani su kusan 350,000 zasu soma jan ragamar yakin da ake yi da 'yan Taliban

Dakarun tsaron NATO 150,000 tare da kayan yaki na zamani ne suke yaki da 'yan Taliban

Kuma yayinda 'yan siyasar kasar ke ta rigima akan sakamakon zabe, yan Taliban din suka kara dannawa sosai zuwa wasu yankunan.

Mr Ghani ya san da cewa zasu dogara ne akan tallafin sojojin Amurka a shekaru masu zuwa. Kuma ba kamar wanda ya gada ba, Mr Ghani ya ce zai sanya hannu akan yarjejeniyar samar da tsaro tare da Washington, wacce ta jima ba tare da an sanya hannu akanta ba, wacce kuma zata tabbatar da cewa akalla wasu dakarun kasashen Turai sun zauna a kasar

A tattauna ko kada a tattauna?

Wani babban kwamitin tsaro ne ke sa 'ido game da tattaunawa tare da 'yan Taliban.

Ashraf Ghani ya ce za a warware rikicin kasar ta hanyar masalaha, amma sai dai ya gaji wani shirin samar da zaman lafiya tare da 'yan Taliban wanda bai je ko'ina ba.

An kasa samun nasarar yunkurin kafa wani ofishin siyasa ga kungiyar Taliban a Qatar, kuma ga alamu sakin fursunonin Taliban bai yi wani tasirin azo a gani ba wajen kawo yarda tsakanin gwamnati da shugabannin masu tayar da kayar baya.

'Yan Afghanistan da dama na da shakkun cewa shirye- shiryen Mr Ghani zasu kawo wani canji.

'Yan Taliban na yiwa Ashraf Ghani da kuma Abdullah Abdullah kallon 'yan barandar Amurka, irin kallon da suke yi wa Hamid Karzai.

Kuma abinda ke faruwa a kasa yanzu na nuna cewa yaki 'Yan Taliban kawai suka sa a gaba amma ba tattaunawa ba

Hakkin mallakar hoto AP

Me zai iya yi game da matarsa?

Ashraf Ghani na fuskantar wata matsala idan aka zo maganar rawar da matarsa 'Rula' zata taka da kuma matsayinta a nan gaba

Rula Ba'amurkiya ce 'yar kasar Labanon, kuma sun hadu ne a shekarun 1970 a lokacin da suke karatu a jami'ar Amurka dake Beirut.

Matan shugabannin Afghanistan dai ba su cika fitowa ba. Amma a wannan karon ga alamu abubuwa za su canza.

Rula Ghani ta taba fitowa a bainar jama'a a wannan shekarar lokacin da take magana yayin daya daga cikin gangamin yakin neman zaben mijinta.

Kuma fitowarta ta sa mata masu fafutuka tunanin cewa bai wa matar sabon shugaban- kasar rawar da zata taka a gwamnati, ka iya yin tasiri mai alfanu akan rayuwar mata.

Amma sai dai abinda ba a sani ba shi ne, wacce irin rawa zata taka a wata al'umma mai ra'ayin rikau, wacce kuma maza suka yi kakagida a cikinta, sannan kuma ko mijinta zai so ta taka wata rawar?