Matasan da suka kashe liman na dakon Hauni

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana yawun samun rikici a yankin Kashgar tsakanin dakarun tsaro da 'yan Uighur

Kafofin yada labaran kasar China sun ce an yanke wa wasu matasa biyu hukuncin kisa, wani guda kuma daurin rai da rai saboda kashe limamin babban masallacin kasar, Sheikh Jume Tahir.

An kashe Sheikh Jume Tahir ne wanda gwamnatin kasar ta nada don jagorantar masu ibada a masallacin da ke birnin Kashgar a can yankin yammacin kasar mai nisa a watan Yuli.

Kotun da ta yanke hukuncin ta ce gungun matasan da aka samu da alhakin wannan aika-aika suna da tsatsaurin ra'ayin addini.

An ce 'yan sanda sun bindige da dama daga cikin wadanda ke da hannu a lamarin, lokacin farautar wadanda suka kashe limamin.

Kashgar na cikin lardin Xinjiang da ke arewa maso yammacin China, yankin da ake yawan samun rikici da fafatawa tsakanin dakarun tsaro da musulmi 'yan kabilar Uighur.